Bayan kashe halifa na uku Usman bin Affan da wasu gungun musulmai suka yi wadanda ba su amince da yadda yake gudanar da mulkinsa na nuna son kai da fifita danginsa ba, sai al'umma ta dace a kan yiwa Imam Ali (a.s) mubaya'a a matsayin jagora. Hakika mutane sun yiwa Imam ca, sai dai ya mayar da martani a kan matsayin na su da cewa: "Ku bar ni ku nemi wanina"(1).
Imam Ali (a.s) ba ya daga cikin irin wadanda mukami ke rudarwa kuma kujerar (halifanci) ke tsolewa ido ta yadda zai gaggauta amsawa mutane, domin mulki (a matsayinsa na mulki) bai kai darajar fiffiken sauro ba a wajensa, kamar yadda ya sha nanata haka a wurare da dama; ya sha jaddada cewa jagoranci ba wani abin ambato ba ne a wajensa matukar ba za a yi amfani da shi wajen tsayar da gaskiya da kawar da bata ba.
Daga karshe dai, bayan nacewar da al'umma ta yi a kan masa mubaya'a, Imam Ali (a.s) ya amince, to sai dai ya kafa wasu sharuddan kafin ya karbi halifancin. Ga wadannan sharudda kamar haka:
"Ku sani cewa lallai ni in na amsa muku, to kuwa zan tafi da ku kan abin da na sani, ba zan saurari zance mai zance da zargin mai zargi ba(2)".
Da wannan bayani, Imam (a.s) na so ne ya tafi da su a kan abin da ya sani daga Musulunci, ba bisa son zukatan wasu ko bisa abin da ke tabbatar da maslahar wasu ba; a wani gurin yana cewa:
"Kuma lokacin da aka ba ni gwamnati sai na duba Littafin Allah da abin da aka sanya mana kuma aka hore mu da shi na hukunce-hukunce, sai na bi su; da abubuwan da Annabi (s.a.w.a) ya sunnata, sai na yi koyi da su.(3)".
Nan da nan al'umma ta gaggauta mika wuya ga sharuddansa, ta kuma mika hannun yi masa bai'a da biyayya, shi kuma ya amsa bukatarta don fuskanci ayyukansa na jagorancin al'umma a fagagen tunani da aiki. Imam (a.s) ya bayayya dalilan da suka sa ya amsawa mutane, inda ya ce:
Ya Allah Ka san cewa abin da ya zo daga gare mu bai kasance rige-rigen mulki ba, ba kuma neman abin duniya ba ne; sai dai don mu bi dokokin addininKa, mu kuma kawo gyara a cikin garuruwanKa, ta yadda wadanda ake zalunta daga bayinKa za su aminta, kuma a tsayar da abin da aka watsar na dokokinKa(4)".
Hakika Imam Ali (a.s) ya dora tafarkin hukumarsa a bisa asasin kalubalantar matsaloli a fagage masu zuwa:
1- Fagen Siyasa
Imam Ali (a.s) ya iyakance siffofin gwamnoni da ma'aikatan gwamnati, wadanda Musulunci ya dora su don gudanar da harkokin al'ummar Musulmi; a bayanin da ya fitar yana cewa:
"Lallai ba ya kamata majibinci a kan rayuwa, jinanai, ganimomi da hukunce-hukunce kana kuma jagoran Musulmi ya zama: marowaci, don sai handamarsa ta zama ciki dukkiyoyinsu. Haka (ba ya kamata ya zama) jahili, don sai ya batar da su da jahilcinsa. Haka (ba ya kamata ya zama) mugu don sai ya yanke su da muguntarsa. Haka (ba ya kamata ya zama) mai fifitawa ba da dalili ba, don sai ya riki wasu mutane ban da wasu. Haka (ba ya kamata ya zama) mai karbar rashawa a hukunci, don sai ya tafi da hakkok. Haka (ba ya kamata ya zama) mai watsi da sunnoni, don sai ya halakar da al'umma(5)".
2- Fagen Tattalin Arziki
Imam (a.s) ya yi watsi da duk nau'o'in bambance-bambance wajen rabon dukiya ga mutane, yana mai tabbatar da cewa tsoron Allah da gabatuwa a Musulunci da jihadi da zama Sahabin Manzon Allah (s.a.w.a) wasu al'amurra ne da ba sa ba masu su wasu martabobi ko su bambanta su da sauran mutane a duniya; maimakon haka, wadancan siffofi suna da ladaddakinsu ne a wajen Allah a gobe lahira; kuma duk wanda ke da wani kasau daga gare su, Allah ne Zai dauki nauyin biyansa. Amma a duniya, mutane duk daya suke wajen hakkoki na dukiya, haka a gaban hukuncin Musulunci da cikin wajibai da takalifofin shari'a.